Bukin cikar Najeriya shekaru 51

Sauti 20:43
Dr Nnamdi Azikiwe Shugaban farar hula na farko a Najeriya
Dr Nnamdi Azikiwe Shugaban farar hula na farko a Najeriya RFI

A ranar 1 ga watan Octoba ne Najeriya ke bukin cika shekaru 51 da samun ‘yancin kai daga turawan Ingila na mulkin mallaka.A cikin shirin “Duniyarmu A Yau”, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wasu ‘Yan Jarida da ke sa ido ga lamurran yau da kullum a Nijeriya domin diba ci gaban da aka samu, da kuma matsalolin da ke addabar kasar.