Afghanistan-Fransa-Amruka

daruruwan mutane sun gudanar da zanga zangar kishin islama a Afghanistan

Daruruwan Mutane ne suka gudanar da zanga zanga a kasar Afghanistan, dan nuna bacin ransu da zanen da mujallar Charlie Hebdo ta buga a Faransa, wanda ya ci zarafin addinin Islama.

تظاهرات ضد آمریکایی در جلال آباد- جمعه ٢٤ سنبله/ ١٤ سپتامبر ٢٠١٢
تظاهرات ضد آمریکایی در جلال آباد- جمعه ٢٤ سنبله/ ١٤ سپتامبر ٢٠١٢ REUTERS/ Parwiz
Talla

Akalla dalibai 300 suka shiga zanga zangar a birnin Kabul, inda suka dinga kalamun batanci kan kasar Faransa da Amurka, a unguwar da Yan kasahsen Tuari suke da zama.

A wani bangaren garin kuma, wasu daruruwan mutane sun taru akan wata gada, inda suma suka gudanar da tasu zanga zangar, sai dai duk an gudanar da su cikin lumana.

Ana ganin wanna zanga zanga a matsayin wani somin tabi, kan abinda zai faru gobe, ganin yadda wallafa zanen ya batawa al’ummar Musulmin duniya rai.

Tuni kasar Faransa ta dauki tsaurararn matakan tsaro, kan ofisoshin Jakadancin ta a kasashe 20 da tace suna fuskantar barazana, tare da rufe makarantu ta.

Kasar Pakistan ta mayar da gobe juma’a a matsayin ranar hutu, dan girmama Manzan Allah wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi.

Rahotanni daga Islamabad na kasar Pakistan na cewa mutane akalla 50 suka sami munanan raunuka a yau yayin wata zanga-zangan nuna rashin amincewa da batancin da aka yi wa musulmi a fadin duniya.

A bangare daya kuma, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ban Ki Moon, ya bayyana fim din da aka yi a Amurka, a matsayin abin kunya, inda yace mutane suna wuce gonad a iri, wajen fadin albarkacin bakin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI