Bakonmu a Yau

Bakonmu a yau: Malam Sani Inuwa Adam

Sauti 03:12
Sojojin sa-kai da ke taimakawa dakarun Iraqi wajen yaki da Mayakan da suka karbe ikon biranen arewacin kasar.
Sojojin sa-kai da ke taimakawa dakarun Iraqi wajen yaki da Mayakan da suka karbe ikon biranen arewacin kasar. REUTERS/Alaa Al-Marjani

Rahotanni daga kasar Iraqi na nuna cewa kasar na fama da babbar matsalar tsaro tun bayan da mayakan sa kai da ake alakantawa da ‘yan Sunni suka kwace wasu yankunan kasar. Yanzu haka rikicin ya fara jan hankun kasashen duniya, inda Amurka da kasar Iran ke yunkurin shawo kan rikicin. Kan haka Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Malam ISani Inuwa Adama na Kwalejin koyar da Shari’a a Jihar Kanon Najeriya.