Mutane 30 sun mutu, wasu 600 sun bata, sakamakon a zaftarewar kasa a Guatemala.
Wallafawa ranar:
A kalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a kasar Guatemala a yayinda wasu sama da 600 suka bata sakamakon zaftarewar kasa da ta rutsa da daruruwan gidajen zaman jama’a dake kusada babban birnin kasar
Yanzu haka dai sama da masu aikin ceto 500 ne, ke ci gaba da kokarin tono wadanda hadarin ya rutsa da gidajensu, bayan da aka dakatar da aikin ceton a daren jiya juma'a
Hadarin dai ya faru ne, tsakanin daren shekaranjiya Alhamis zuwa safiyar jiya juma’a, a wani wuri mai tazarar kilo mita 15 gabashin Santa Catarina Pinula babban birnin kasar ta Guatemala
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu