Hotunan Jana'izar Marigayi Dan Masanin Kano Maitama Sule

Dan Masanin Kano, Dr. Yusuf Maitama Sule a Lokacin da yake Hira da RFI Hausa RFIHausa/bashir

An yi Jana’izar Marigayi Dan Masanin Kano Alhaji Maitama Sule a garin Kano wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Litinin 3 ga watan Yuli a Kasar Masar. Dubban Mutane ne suka halarci Sallar Jana’izar fitaccen dan siyasar na Najeriya wanda tsohon jekada ne a Majalisar Dinkin Duniya. Rahotanni sun ce an binne shi ne a Makabartar Kara da ke Kofar Mazugal a garin Kano.

Talla