Hotunan murnar kawo karshen mulkin Mugabe a Zimbabwe

Al'ummar Zimbabwe na bikin murnar kawo karshen mulki Mugabe a kan titunan kasar REUTERS/Siphiwe Sibeko

Al'ummar Zimbabwe na ci gaba da murnar kawo karshen mulkin Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 akan karaga. Mugabe ya yi murabus ne bayan ya sha matsin lamba daga sojoji da kuma al'ummar kasar. An zargi Mugabe da kokarin bai wa matarsa Grace Mugabe damar gadon shugabancin kasar, abin da ya sa ya kori mataimakinsa, Emmerson Mnangagwa. Koran Mnangagwa ne ya tayar da guguwar ganin cewa Mugabe ya sauka.

Talla