Hotunan yadda Musulmi suka yi Sallah a sassan duniya karkashin matakan dakile corona

Daidaikun Musulmin da suka samu damar gudanar da Sallar Idi karama a Masallacin Harami dake birnin Makkah. AFP

Ranar Lahadi 24 da watan Mayu na shekarar 2020, wanda yayi daidai da 1 ga watan Shawwal shekara ta 1441 bayan hijirar Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wa Sallam, mafi akasarin al’ummar Musulmi a sassan duniya da suka hada kasashen Asiya, Gabas ta Tsakiya ciki harda yankin Falasdinu, Turai da ma kasashen Afrika suka yi bikin Sallar Idi karama bayan cika kwanaki 30 na watan Azumin Ramadana. Bikin Sallar karama ta bana ta zo ne cikin yanayi na matakan killace jama’a da kuma takaita zirga-zirga gami da hana taron jama’a saboda dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla