IMF

IMF ta damu dangane da karafkiyar darajar kudade

Nacho Doce/Reuters

Shugaban bankin ba da lamuni na duniya IMF Cif Dominique Strauss Kahn ya ce yana cikin damuwa matuka dangane da karafkiyar darajar kudade da ke wakana tsakanin kasashen dake sarrafa linzamin tattalin arzikin duniya. A yau Alhamis ne kungiyar tarayyar Turai EU ta yi gargadin cewa karfin darajar kudin Yuro ka iya yin zagon-kasa ga kokarin farfado da tattalin arziki.Ya ce darajar kudin Yuro ta yi tashi gwauron-zabi zuwa kusa da Dala 1.40, yayin da ita kuma Dala ta rufto a karon farko cikin shekaru 50.Ya yi gargadin cewa meyiwa kasashe sai sun dauki matakai a cikin gida, maimakon su zuba wa kasashen duniya idanu, ta hanyar rage darajar kudadensu, don bunkasa fitar da kayayyakinsu.Tuni dai hukumomin kasar Japan suka dakatar da hauhawar darajar Yen a wuri guda, Brazil ma na kokarin daukar irin wannan mataki kan kudinta na Real, kasancewar darajar Dala na ci gaba da faduwa ne bisa fargabar rashin tabbas.