Kasuwanci

Kudaden Da Nigeria Ta Kashe Wajen Gudanar Da Zabukan Shekarar 2011

Sauti
Prof. Attahiru Jega
Prof. Attahiru Jega

A wannan shirin za mu duba irin makudan kudaden da gwamnatin tarayyar Nigeria ta baiwa hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC, don gudanar da zabukan kasar na shekarar 2011. Ko kwalliya za ta biya kudin sabulu game da wadannan kudaden? Tabayar da shirin ya nemi jin amsar ta ke nan. Shirin ya sami ganawa da bangarori daban daban, da ke da ruwa da tsaki a zabukan kasar, kama daga jami’an hukumar zaben ta INEC, ‘yan siyasa da ake damawa da su a fagen siyasar kasar da ma talakawa da ke sa ido kan yadda hukumomin kasar ke amfani da kudaden nasu. A yi saurare lafiya.