Kasuwanci

Tsarin Banki Na Islama

Sauti 10:00

Alkalumman tattalin arzikin kasa da kasa da jami'ar Havard dake Amurka, na nuna cewa tsarin bankin Islama daya samo asali daga tsakiyar wannan karnin, nada rassa a kimanin kasashe 100 na dinuya. Jimillar wadanan bankunan na Islama dake da jarin sama da dala miliyan dubu 300a hannun jari da kaddarori, na samun habakar akalla kashi 10-15 cikin 100 kowacce shekara a huddar karbar ajiya da bada bashin da ba kudin ruwa akai.Koda yake tsarin bankin na Islama na cigaba da samun karbuwa a Amurka,kasashen turai da yankin Asia,shelar babban bankin Nigeria na bada lasisin wannan rukunin bankin, na haddasa zazzafar muhawara a bangaren tattalin arziki da zamantakewa.A nasa bangare dai babban bankin na Nigeria CBN,na cewa sai da aka bi sharuddan da dokoki suka shimfida,kafin cimma shawarar bada lasisi fara bankin na Islama da bada tabbacin cewa gudanar wannan bankin ba zai shafi huddar sauran bankunan dake hidimar kasuwanci a Nigeria ba.Babban bankin na CBN ya bada misalai kan yadda wanann bankin na Islama ke gudanar a yawancin kasashe na duniya ba tare da wata matsala ba.Sai dai kuma duk da wannan tabbacin daga babban bankin na CBN,kungioyin addini da wani bangare na tattalin arziki na cigaba dakafa-kafa da yin kasedi kan tasirin bankin na Islama a yanayin zamantakewa da tattalin arzikin Nigeria.