Kasuwanci

Rahoto Kan Tashin Farashin Siminti A Najeriya

Sauti 10:04

Farashin Siminti yayi tashin gwauron zabbi a 'yan kwanakin nan a tarayyar Najeriya, inda a cikin kasa da wata daya farashin jaka daya yakai naira dubu ukku. Kamin tashin farashin dai ana saida jaka dayane akan kudi naira dubu daya da dari shida da hamsin zuwa dubu daya da dari bakwai. Bisa wannan ne wakilin mu a Sokoto Faruk Muhammad Yabo, ya hada mana wannan rahoton na musamman.