Kasuwanci

Dambarwar Bashin Amurka Da Tasirin Sa

Sauti 10:00
© Reuters

Bayan tada jijiyoyin-wuya tsakanin shugaba Barack Obama da 'yan jam'iyyar Republican dake da rinjaye a majalissar wakilai,daga karshe dai bangarorin biyu sun amince da daga adaddin bashin da Amurka zata iya chi daga Dallar Trillion 14 zuwa Dalla Trillion 16. Watau kari wasu Dalla Trillion 2 ke nan,da kuma zabtare wani kaso kwatankwacin wannan karin kan abinda gwamnati ke batarwa kowacce shekara.Sai dai kafin cimma wannan yarjejeniyar wannan batu na tattalin arziki,ya rikide zuwa na siyasa,inda jam'iyyun biyu dake mulki a Amurka watau Democrats da Republicans,suka yi ta musayar zazzafan kalamai kan wannan batu na bashi da yadda za'a bullo masa musamman kafin ranar 2 ga watan Agusta, ranar da hukumar tara kudade ta Amurka tayi kasedin cewa gwamnati zata tsiyace wajen sauke nauyin dake kanta!A yayin da ake tabka muhawara kan wannan batu a kasar ta Amurka,kasuwannin duniya musamman na darajar hannun-jari,sun fadi a kasashen China, Japan da WallStreet.Daga kasashen Girka zuwa Italiya,Spain,Portugal da ta baya-bayan nan watau Israila, ana cigab da samun jerangiyar jama'a dake machi kan tituna kan rashin aikin yi,zaman kashe-wando da kuma tsadar rayuwa,yanayin da masana ke cewa bai rasa nasaba da tabarbarewar tattalin arzikin Amurka.Shin wadanne dalilai suka kai ga jefa tattalin arzikin na Amurka cikin tsaka-mai-wuya, kuma menene tasirin wannan matsalar ga kasuwannin duniya? Wannan shine abinda shirin Kasuwa-Akai-Maki-Dole na wannan yasa gaba.