'Yan kasuwa na son a bude kasuwar Shanu a Maiduguri

Sauti 10:08
Barazanar Satar Shanu da hare haren Boko Haram ya sa aka rufe kasuwannin cinikin Dabbobi a Borno
Barazanar Satar Shanu da hare haren Boko Haram ya sa aka rufe kasuwannin cinikin Dabbobi a Borno REUTERS/Stringer

Kasuwannin Shanu na ci gaba da kasancewa a rufe a Jihar Borno da ke Najeriya matakin da da gwamnati ta dauka saboda barazanar Boko Haram, Shirin Kasuwa a kai maki dole ya yi dubi dangane da matakin da kuma yadda hakan ya shafi rayuwa da tattalin arzikin wadanda suka dogara da sana'ar sayar da dabbobi a jihar Borno.