Muhimmancin sanar bola-jari a Najeriya

Sauti 10:47
Sana'ar bola-jari ta samu karbuwa a wajen matasa musamman a yankin arewacin Najeriya
Sana'ar bola-jari ta samu karbuwa a wajen matasa musamman a yankin arewacin Najeriya In Pictures Ltd./Corbis via Getty Images)

Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon tare da Mohammed Sani Abubakar ya tattauna ne kan muhimmancin sana'ar bola-jari, in da matasa ke yawo kan shara don kalato wasu kayayyakin da aka wurgar saboda lalacewa ko rashin amfaninsu kamar kwalba, gwangwani ko kuma karfe. Shirin ya ji ta bakin wani matashi da ya ce, sana'ar bola-jari ta rufa ma sa asiri domin kuwa ya mallaki gidan kansa, ya kuma yi aure, sannan kuma ya biya wa mahaifiyarsa kujerar Makka duk dai a cikin wannan sana'a.