Najeriya da Nijar za su kafa aikin gina matatar man fetur a Katsina (2)

Sauti 11:06
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Nijar  Mahammadou Issoufou a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Nijar Mahammadou Issoufou a Abuja tamtaminfo.com

Shirin Kasuwa a kai Mi Ki Dole na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora ne kan na makon jiya, in da ya tattauna game da shirin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na gina matatar man fetir a jihar Katsina da kuma sinfida bututun da zai rika janyo man daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.