Kasashen Turai na zuba jari a kasashen Afrika

Sauti 10:19
Theresa May ta Birtaniya da  Muhammadu Buhari na Najeriya a Abuja
Theresa May ta Birtaniya da Muhammadu Buhari na Najeriya a Abuja https://politicsngr.com

Shirin Kasuwa a kai miki Dole na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan yadda kasashen Turai ke ci gaba da kokarin zuba jari a kasashen Afrika a dai dai lokacin da China ta yi wa nahiyar kamun-kazan-kuku. Ko a baya bayan Theresa May ta Birtaniya da Angela Merkel sun ziyarci nahiyar, in da kowacce daga cikinsu ta halarci Najeriya ganin muhimmancin kasar a Afrika ta fuskar kasuwanci.