IMF

Rikicin China da Amurka na shafar arzikin duniya-IMF

Shugabar Asusun Lamuni na Duniya, Christine Lagarde
Shugabar Asusun Lamuni na Duniya, Christine Lagarde 路透社

Asusun lamuni na duniya ya ce rigimar kasuwancin da ake yi tsakanin China da Amurka za su iya shafar hasashensa na habakar tattalin arzikin duniya tsakanin shekara ta 2018 zuwa 2019.

Talla

Rahotan watanni uku-uku da asusun na IMF ke fitarwa, ya ce rikicin kasuwancin zai yi mummunan tasiri ba wai ga tattalin arzikin kasashen biyu kawai ba, har ma da na sauran kasashen duniya sakamakon sabon haraji da kuma zaftare kudaden da Amurka ke kashewa sabanin yadda asusun ya yi hasashe tun da farko.

Asusun ya ce, tattalin arzikin duniya zai habaka da kashi 3.7 cikin 100, abin da ya yi kasa da hasashensa na watan Afrilu, wato kashi 3.9.

Tun a makon jiya ne, shugabar Asusun, Christine Lagarde ta ce, yanayin tattalin arzikin duniya na sauyawa, abin da ya janyo hankulan hukumomin tattalin arziki na kasashen duniya don tattaunawa kan makomar tattalin arikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.