Isa ga babban shafi

Amurka da China sun kawo karshen yakin kasuwanci

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping. 网络图片
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinpin sun cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin kasuwanci da ya kullu tsakaninsu, a wata ganawa da suka yi a jiya Asabar gabannin rufe taron kungiyar kasashen G20 a Argentina.

Talla

Muhimman batutuwan da yarjejeniyar ta kunsa su hada da cewa, Trump zai dakatar da shirinsa na kakaba harajin kashi 25 kan kayayyakin da China ke shigarwa Amurka da darajarsu ta kai na dala biliyan 200, wanda a da zai soma aiki a farkon watan Janairu.

Ita kuma China za ta sayi kayayyaki masu yawa daga Amurka daga fannonin noma, makamashi, da kuma masana’antu, domin rufe gibin da huldar kasuwancinsu ya fuskanta, a dalilin yakin kasuwanci da suka kwashe watanni suna yi.

Yarjejeniyar ta fayyace cewa, rashin dabbaka kudurorin da shugabannin biyu suka cimma a cikin wa’adin watanni 3, na nuni da cewa za’a ci gaba da fafata yakin kasuwancin da ya kullu a tsakaninsu.

Zalika shugaba Trump da Xi Jing Pin za su soma tattaunawa akan batutuwan da suka shafi musayar fasahar kere-kere, yakar laifuka ta shafukan yanar gizo da kuma ayyukan gona.

A wani labarin kuma takardar bayan taron na G20 ya bayyana Amurka a matsayin saniyar ware tsakanin kasashen 20 masu karfin tattalin arziki, dangane da batun yarjejeniyar rage dumamar yanayi, abinda ke nuni da cewa har yanzu Amurkan na kan bakanta na janyewa daga cikin yarjejeniyar ta 2015 duk da kokarin shawo kanta da takwarorinta ke yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.