OPEC-Tattalin arziki

OPEC za ta rage yawan man da take fitarwa

Tambarin kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur.
Tambarin kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur. © Reuters

Manyan kasashe masu hakar mai a duniya sun amince su dan kara bunkasa adadin gangan mai da suke samarwa daga watan Agusta, bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi watsi da wata yarjejeniyarsu a farkon wannan watan.

Talla

Taron kasashen kungiyar OPEC da abokansu da ba sa cikin kungiyar sun amince su fara samar gangan mai dubu 400 a kowace rana daga watan Agusta mai kamawa don taimaka wajen bunkasa farfado da tattalin arzikin duniya yayin aka fara samun saukin annobar korona da ta jefa fannin cikin wani yanayi.

A farkon watan Yuli, mambobin OPEC da kawayenta sun gaza cimma matsaya dangane da adadin gangan Mai da kasashe ya kamata su samar, sakamakon rikici tsakanin Saudiyya dake kan gaba a harkar da kuma makwabciyarta Hadaddiyar Daular Larabawa.

Tun daga watan Mayu, rukunin mambobi kungiyar 23, ciki har da kasar Rasha, sun bukaci kara adadin da kadan-kadan, bayan da suka sauka da shi fiye da shekara guda lokacin da cutar korona ta addabi duniya.

Manufar dai  ita ce komawa ga adadin da suke samarwa kafin bullar annobar sannu a hankali, kan kasa da ganga miliyan 5 da dubu 800 da suke samarwa yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.