Najeriya - OPEC

Najeriya za ta amfana da shirin OPEC na gina sabbin matatun mai

Alamar OPEC da aka zana gabanin wani taro na yau da kullun tsakanin mambobin kungiyar a Algiers dake Algeria, Satumba 28, 2016
Alamar OPEC da aka zana gabanin wani taro na yau da kullun tsakanin mambobin kungiyar a Algiers dake Algeria, Satumba 28, 2016 REUTERS - Ramzi Boudina

Kungiyar kasashe masu arzikin mai OPEC ta ce Najeriya da sauran kasashe masu tasowa za su amfana da kimanin dalar Amurka biliyan 450 da za a kashe wajen gina sabbin matatun mai da kuma bunkasa ayyukan wadanda suke da su.

Talla

Kungiyar kasashen masu arzikin man fetur ta bayyana haka ne ta hannun babban sakataren ta Sanusi Barkindo, yayin gudanar wani taro kan makamashi na Afirka da aka yi a birnin Cape Town dake Afirka ta Kudu a ranar Talata.

OPEC ta ce zuba jarin wani bangare a karkashin gagarumin shirin da take jagoranta, da ya kunshi dala tiriliyan 1 da biliyan 500, da za a zuba a bangaren mai da iskar gas domin bunkasa fanonin daga 2021 da muke ciki zuwa shekarar 2045.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI