Belgium

Prime Minista Ya Bada Takardan Ajiye Aiki

Prime Ministan kasar Belgium Yves Leterme ayau ya mika takardan ajiye aikinsa sakamakon janye goyon bayan Gwamnatin hadin kan kasar, da wata Jamiyya tayi. Saidai kuma Sarki Albert 11 bai bayyana cewa zai karbi takardan ajiye aikin ba ko kuma a’a, kamar yadda wata sanarwa daga fadar Sarkin ke nuna wa.Jamiyyar VLD ce dai ta fita daga cikin Gwamnatin hadin kan na jamiyyu biyar, alamarinda yasa Prime Ministan ajiye aiki ba shiri.Tun da wuri ayau saida Sarki Albert 11 yayi wani taron gaggawa da Prime Ministan mai barin gado.Sarkin ya fada cewa wannan takaddana ko shakka babu zai shafi matsayin kasar aKungiyar Tarayyar Turai.