FARANSA

Ma'aikatan Faransa Sunyi Bore

Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy
Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy rfi

Dubban maaikatan kasar Faransa ayau sun gudanar da zanga-zangan lumana , da jerin gwano a tituna domin nuna adawarsu ga matakan da Shugaba Nicholas Sarkozy ke dauka na kara wa’adin shekaru don ajiye aiki.Kuriar jin ra’ayoyin jamaa da aka gudanar na nuna cewa yawancin ma’aikata basa bukatar Shugaban yayi wasu sauye sauyen tsarin ayyukan maaikata.Duk da ruwan sama da akayi ta sharawa a birnin Paris ma’aikatan daga wasu sassan kasar sunyi dafifi domin shiga zanga- zangan lumanan.Kasashen dake makwabtaka da kasar Faransa sun bayyana matakai daban daban don tsuke bakin aljihu, amma Gwamnatin Sarkozy na taka tsantsan ganin cewa akwai raguwar farin jinin Shugaban , ga kuma batun zabe da yake fuskanta nan da shekaru biyu.