Isra'ila

Blair ya soki kawanyar Gaza da Isra’ila keyi

Tsohon Pri Ministan Britaniya, Tony Blair
Tsohon Pri Ministan Britaniya, Tony Blair REUTERS/UKBP

Tsohon Pri Ministan Britaniya, Tony Blair, ya soki matakin da kasar Isra’ila ke dauka, na cigaba da kawanya wa Yankin Gaza, inda ya baiayan matakin a matsayin koma baya.Blair ya shaidawa shugabanin Isra’ila cewar, cigaba da hana mutanen Yankin damar samun kayan more rayuwa, ba zai taimake sub a.Tsohon Pri Ministan ya baiyana tsoron sa cewar, matakin na jefa shakku kan mutanen dake Gaza, na shirin sasantawa da Isra’ila, wajen samun kasashe biyu, kafada da kafada.Kasashen duniya da dama, tare da Majalisar Dinkin duniya, sun yi Allah wadai da matsayin Isra’ila kan Yankin Gaza, da kuma harin da ta kaiwa tawagar kayan agaji.