Faransa-Isra’ila-Palesdinawa

Sarkozy ya bukaci Isra’ila ta amince da binciken Majalisar Dinkin Duniya

SHUGABAN Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya bukaci Pri Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ya amince da shirin Majalisar Dinkin Duniya, na kafa kwamitin da zai binciki harin da dakarun kasar suka kaiwa tawagar jiragen agaji zuwa Gaza.A tattaunawar da sukayi ta waya, shugaba Sarkozy ya kuma bukaci Israela ta kawo karshen kawanyar da take wa Gaza, inda ya bayayana shirin kasar na sa ido a duk wani kayan agajin da za’a kai Gazan.Isra’ila dai taki amincewa da shirin gudanar da binciken, kamar yadda Jakadan ta a Amurka, Michael Orien ya bayyana, inda yake cewa, matakin yayi dai dai da na kasar Amurka, wanda ba zata amince da bincike kan yadda sojin ta ke gudanar da aiki a Afghansitan ba. Kasar Turkiya, da aka kashewa mutane tara, tace zata dauki duk matakan da suka dace, wajen ganin an gudanar da bincike, inda ta bayyana matakin Isra’ilan, a matsayin amsa laifi.