FARANSA

Frenshi da Qatar kan rikicin iyaka Djibouti da Eritrea.

AFP/Eric Feferberg

      Kasar Franshi ta nuna karfafa gwiwa ga kasar Qatar kan shawo matsalar iyaka da ake fuskanta, tsakanin kasar Djibouti da ta Eritrea.Shugaban kasar Franshi Nicolas Sarkozy shi da kanshi ne ya furuta hakan a yau.       A yanzu haka dai ,wanan yanki na kumshe da dumbin dakarun kasar Franshi da ke girke domin sa ido kan abubuwan da ke wakana.         Kasar Qatar ta sanar da cewa dakarun kasar Eritrea sun baro yankin da su ke a kasar Djibouti,wanan na nuna wata alama ta samun hanyoyin warware rikicin a cikin sauki.