EU

Ministocin kudaden kasashen Turai sun amince da kudirin kafa asusun tallafi

MINISTOCIN Kudin kasashen Turai
MINISTOCIN Kudin kasashen Turai Pjhoto: Eric Vidal/Reuters

MINISTOCIN Kudin kasashen Turai, sun amince da kafa wani asusun Euro Biliyan 440, dan kai dauki wa duk wata kasa dake fuskanatar matsalar tattalin arziki.Pri Ministan Luxembourg, Jean Claude Juncker, yace matakin da zai taimaka gaya, wajen kaucewa durkushewar tattalin arziki, da kuma kare darajar kudin Euro, wanda ke cigaba da shan kashi.Juncher yace, ya zuwa yanzu akwai sauran kasashen da ake saran zasu kamala sanya hannu, kan kudirin kafa asusun, amma wata majiya tace, tuni kasar Jamus ta rattaba hannu akai.