FARANSA

Yau za’a fara shari’ar zargin mummunar al’mundahana

Photo:Benoit Tessier/Reuters

YAU ne ake fara shari’ar Jerome Kerviel, wani Dan kasuwa a kasar Faransa, wanda ake zargi da wasu hada hadan da suka sabawa ka’ida, abinda ya kaiga Banki Societe Generale, yayi asarar Euro biliyan biyar.Bankin na zargin Kerviel ne da kokarin durkusar da shi, wajen sayen hannayen jari, ba tare da sanin Bankin ba.Zargin dai na dauke da hukuncin shekaru biyar a gidan yari.