Faransa

Shirin Rage kashe kudaden akan jami’an gwamnati

Le Premier ministre, François Fillon (G), en compagnie du ministre du Budget, François Baroin (D), devant l'Elysée. Pour ce dernier le budget 2011 ets «le plus difficile à préparer depuis 30 ans».
Le Premier ministre, François Fillon (G), en compagnie du ministre du Budget, François Baroin (D), devant l'Elysée. Pour ce dernier le budget 2011 ets «le plus difficile à préparer depuis 30 ans». Reuters/Philippe Wojazer

Gwamnati shugaba Nicolas Sarkozy ta kasar Faransa, ta bayyana shirin rage kashe kudade kan jami’an gwamnati tare da saka takunkumi kan duk ministan da ya kashe kudi al’umma ta hanyar data saba ka’ida.A cikin sabon shirin an bukaci ministoci su yi amfani da jiragen kasa, tare da rage yawan masu taimaka musu. A wata wasika da shugaba Sarkozy, ya tura wa PM kasar ta Fansa, François Fillon, ya nemi a rage motoci 10,000 na gwamnati da wuraren ajiya manayan jami’an 7,000 da gwamnati ke biyan kudaden haya.Sarkozy ta kuma soki liyafar shekara shekara ta fadar mulkin kasar Elysée.Wani Dan majalisa na bangaren Yan gurguzu, ya facaccaki kasafin kudin da Sarkozy ya gabatar da cewa, bayi da tasiri wa rayuwan al’umma.