Birtaniya-Amurka

Kamfanin Mai na BP zai samu sabon shugaba

Shugaban kamfanin BP Hayward mai barin gado
Shugaban kamfanin BP Hayward mai barin gado Reuters

Kamfanin mai na BP mallakin kasar Birtaniya, ya tabbatar da cewa shugabansa Tony Hayward, zai ajiye aiki farkon watan Oktoba, tare da maye gurbinsa da Bob Dudley.Dudley wanda zai karfi aiki daya ga watan Oktoba mai zuwa. A cikin hira da wata kafar yada labaran Amurka, ya ce zai mayar da hankali kan tsabtace tekun Mexico na Amurka, inda aka samu lamarin tsiyayan man fetur.Bob Dudley ya zama dan kasar Amurka na farko da zai shugabanci kamfanin na BP, inda yanzu haka kamfanin ya ware kudaden da sukakai dala bilyan 32, saboda cike asarar da kamfanin yayi a tekun Mexico na kasar ta Amurka.