Slovakia

Dan Bindiga Ya Kashe Mutane Bakwai A Slovakiya

Taswirar kasar Slovakiya
Taswirar kasar Slovakiya Rfi HAUSA

Wani dan bindiga dadi yau littini ya yi ta harbin kan mai uwa da wabi a tsakiyar babban birnin kasar Slovakiya, Bratislava inda ya kashe mutane bakwai wasu mutane 14 suka sami munanan raunuka.Wasu ganau sunce mutumin ya hallaka kansa daga bisani.Lamarin ya auku ne a rukunin gidaje na Devinska Nova Ves dake Arewa maso yammacin birnin.Wata ma'aikaciyar  agaji Dominika Sulkova tace yawan mamatan na iya karuwa nan gaba.