Netherlands

Jamian Tsaro Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Zargi shirin Ta'addanci

Hoton filin jiragen sama na Netherlands
Hoton filin jiragen sama na Netherlands rfi

Wasu ‘Yan asalin kasar Yemen  biyu dake zaune a kasar  Amirka na hnnnun jamian tsaron kasar Netherlands bayan sun shiga wani  jirgin sama daga Chicago zuwa Amsterdam da wasu kaya marasa kangado.Ana zargin su ne da mallakan wasu tarkace na take taken kai harin ta’addanci a cikin jiragin saman United Airlines 908.Jamian tsaro dake filin jiragen sama na Amirca sun duba jikin mutanen biyu da naurorin bincike, kuma sun gano kayayyakin da mutanen suka mallaka na kunshe da wasu abubuwa da ake zargi suna da niyyar kai wani hari ne.Daga cikin abubuwan da aka sami mutanen dasu akwai wukake, wani wayan hannu da aka makala shi jikin wani kwalban magani da kuma wasu wayoyin da agogon hannu da aka daure su tare.Jamian tsaron Amirka, nan da nan suka sanar da jamian tsaron kasar Dutch, kuma nan da nan aka sanar da jamian tsaron filin jiragen sama na Schiphol aka kama mutanen.Mutanen sun hada da Ahmed Mohammed Nasser al-Soofi da kuma Hezam al-Murisi.