New Zealand

Mahaka 36 sun salwanta a New Zealand

Wasu mahaka a kofar shiga kofar kamfanin hako ma'adinai yankin Grey a kasar New Zealand
Wasu mahaka a kofar shiga kofar kamfanin hako ma'adinai yankin Grey a kasar New Zealand Reuters

HUKUMOMIN Kasar New Zealand, sun sanar da cewa, wasu mahaka sama da talatin sun salwanta. bayan fashewar Bom da aka samu a mahakar kasar. Kodayake har yanzu ba a tantance musabbabin faruwar al’amarin ba.Magajin garin Yankin Grey, Tony Kokshorn, wanda ya bayyana bakin cikinsa kan hadarin, yace har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.Mahakar dai na daya daga cikin manyan mahakar ma’adinai da ke da rassa Ashirin da biyu a kasar ta New Zealand wacce kuma ke samar da ton din kwal miliyan biyar duk shekara.