Ruwan sama da gurbatar yanayi a yankin gabas ta tsakiya
Wallafawa ranar:
Mumunar guguwa, ruwan sama, tare da dusar kankara, na cigaba da mamaye kasashen da ke Gabashin tekun Mediterranean, da kuma Gabas ta Tsakiya. Rahotanni sun ce, iskar ya nitsar da wani jirgin ruwa, kusa da Isra’ila, abinda ya sa aka hanama jirage ruwa wucewa a mashigar ruwa ta Suez Canal.Har ila yau ,an dakatar da sufurin jiragen sama a Yankin.