Turkiya

An fara sharia wa sojojin Turkiya da ake zargi da yunkurin juyin mulki

Shugaban Turkiya Abdullah Gul yana tattaunawa da sabon babban habsan soja General Isik Kosaner
Shugaban Turkiya Abdullah Gul yana tattaunawa da sabon babban habsan soja General Isik Kosaner

A yau Alhamis a birnin Istambul na kasar Turkiya an fara zaman sauraren shara’ar da ake yiwa wasu yiwa wasu sojojin kasar 200, wadanda suka hada da manyan sojojin bisa zargi da yunkurin kifar da gwamnatin kasar.Wannan shara’a dai na zama babbar barazana ta kai tsaye da ba’a taba gani ba ga sojan kasar ta Turkiya, da babu ruwanta da addini, yunkurin da ake ganin na ci gaba da ja da baya tun lokacin da jam’iyar AKP ta PM Recep Tayyip Erdoga, ta dare kan karagar shugabancin kasar a 2002.Wani alkali ya bude soma zaman sauraren shara’ar ta yau, da tantance sojoji 196 da ake zargi, wadanda gabadayansu suka halarci zaman kotun ba tare da ankwa ba.