Birtaniya
Kotun birnin London ta tabbatar da belin Assange shugaban shafin WikiLeaks
Wallafawa ranar:
A wani zama na tsawon mintina 90 a yau Alhamis madaukakiyar kotun birnin Landon ta kasar Birtaniya, ta bada bellin karar da a ka daukaka, ga shugaban shafin yanar gizon Wikileaks Mai fallasa bayanan sirrin da a ka bashi Julian Assange.Alkalin mai shara’a Duncan Ouselay, ya bayyana cewa, ya bada bellin Julian Assange bisa sharadi jinginar da kimanin Euro dubu 280. Matakin da ba za a daukaka kara a kansa ba.A ranar 7 ga watan nan ne, aka kama Julian Assange dan kasa Austarliya mai shekaru 39 a duniya, bisa bukatar kasar Sweden, dake son mika mata shi domin fuskantar hukumci kan zargin aikata faide a kasar wa wasu mata biyu.