Kosovo

Kungiyar Turai zata binciki zargi da ake wa PM Kosovo Thaci

Prime Ministan Kosovo, Hashim Thaçi.
Prime Ministan Kosovo, Hashim Thaçi. (Photo : AFP)

Kungiyar Kasashen Tarayyar Turai, ta ce zata kaddamar da bincike, kan zargin da akewa Prime Ministan Kosovo, Hashim Thaci, na hannu a safarar sassan jikin bil Adama.Kakakin Babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar, Catherine Ashton, ta ce kungiyar tana daukar batun laifufukan yaki da kuma ta’adanci da girma, saboda haka zata gudanar da bincike akai.Ana samun karin matsin lambar neman sanin gaskiyar abun da ya farau da Trayyar Turai da kasar Amurka wadanda ke mara baya wa ballewar da Kosovo yayi da Sabiya. Tuni gwamnatin Kosovo ta yi watsi da wannan zargi da ake wa PM Thaci, wanda jam'iyyarsa ta samu rinjaye yayin zaben da ya gabata.