FARANSA

Kanfanin Renault a kasar Franshi ,ya dakatar da wasu manyan jami’ai guda 3

Bikin baje koli na motoci kirar Renault
Bikin baje koli na motoci kirar Renault REUTERS/Benoit Tessier

A kasar Franshi, kanfanin kera motoci samfarin Renault ,ya dakatar da wasu manya-manyan jami’an kanfanin guda 3 ,da ake tuhuma da baiyana sirin kanfanin game da sabuwar fusa’ar shi ta fanin kera wasu motoci sanfarin renault sabon salo ,a cikin tsakiyar wanan shekara ta 2011 da kuma ta 2012. An dakatar da jami’an ne kan zargin ba su darata kaidodin sirin kanfanin ba.