Tirana

Mutane 3 sun mutu a zanga-zangar adawa da gwamnatin Tirana

masu gudanar da zanga-zanga lokacin da suke arangama da jami'an tsaro a Tirana
masu gudanar da zanga-zanga lokacin da suke arangama da jami'an tsaro a Tirana Reuters / Arben Celi

Jami’an tsaron kasar Albaniya sun ce mutane 3 ne suka mutu, mutane da dama kuma suka ji rauni sanadiyar wata zanga zanga da al’ummar kasar suka gudanar don nuna adawa da gwamnatin kasar a tsakiyar Tirana babban birnin kasar.Dubun dubatar ‘yan kasar ne suka yi gangami bayan wani kira da Jam’iyyar adawa ta yi na nuna kyama ga gwamnati mai ci ta Fira Minista Sali Berisha.Sai dai kuma zanga-zangar ba a kwashe lafiya ba da Jami’an tsaron bayan tarwatsa gungun masu gudanar da zanga-zangar da barkonon tsohuwa da jami’an tsaron kasar suka yi lokacin da suke jifar su da duwatsu.