Faransa

Tsohon shugaban Faransa Chirac zai fuskani kotu

Da safiyar yau Littini wata kotu dake nan Faransa zata fara sauraron karar da aka shigar na zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa Tsohon Shugaban Faransa Jacques Chirac.Chirack mai shekaru 78 da haihuwa zai kasance na farko cikin tsoffin Shugabannin kasar ta Faransa da aka taba iza keyarsa zuwa gaban kuliya saboda zargin cin hanci a lokacin da ayke magajin gari.Shidai Chirac ana zargin sa ne da anfani da makudan kudaden gwamnati wajen biyan ma'aikatan karya a lokacin da yake Magajin gari tsakanin shekara ta 1977 & 1995.Muddin aka sami hannunsa cikin wannan abun ashsha to kuwa zai kwashe tsawon shekaru 10 a gidan kurkuku da taran kudin Turai Euro dubu 150.Tun kafin yau tsohon Shugaban wanda aka sani da cewa mai kyamar harin da kasashen duniya suka kaiwa kasar Iraki ne, y ace karyan tsiya ake masa, domin lauyoyinsa na zargin akwai batun siyasa a ciki.Yanzu haka dai Jack Chirac na ta kansa ne saboda rashin lafiya irin na tsufa koda yake lauyoyinsa sun nemi alfarman bazai bayyana gaban alkali yau Litinin ba saidai gobe Talata.  

Jacques Chirac tsohon shugaban kasar Faransa
Jacques Chirac tsohon shugaban kasar Faransa Reuters/Benoit Tessier