Faransa

Kotu ta fara sauraron karar da aka shigar da tsohon shugaban Faransa Chirac

Tsohon shugban Faransa  Jacques Chirac.
Tsohon shugban Faransa Jacques Chirac. AFP

An soma shara’ar Jaques Chirac, tsohon shugaban kasar Faransa da ake tuhuma da yin anfani da ma’aikata na jebu domin daukar wasu kudade a lokacin da ya ke magajin garin Paris babban birnin kasar. Bayan dai da kariyar tsohon shugaban kasar Jacques Chirac ta kare, abu na farko da ya soma da shi, shi ne sallama da gurfana a gaban kotu kan tuhumar da ake masa na laulaye wasu mukudan kudade a lokacin da ya ke magajin garin babban birnin Paris. Hakan ya wakana ne ta hanyar shirya sunayen wasu ma’aikata na jebu a cikin shekarun 1990. A yau dai ana ganin da wuya tsohon shugaban kasar ya halarci zaman kotun da kansa. Duk da haka ya kassance shugaba na farko da ya jagoranci kasar ta Faransa da irin wannan lamari ya fada kansa.Lauyoyin sauran mukaraban tsohon shugaban su nemi da a sake duba wannan lamari kan mahimmanci abubuwan da su ka cancanta kuma kan ka'ida.Babban alkali mai shara’a Dominique Pauthe, ya sanar da cewa a yau Talata da karfe daya da dari na rana za a sanar da abun da kotun ta tsaida kan yadda za a gudanar da shara’ar.