Faransa

Kotun Faransa ta Jingine shari’ar tsohon shugaba Chirac

Kotun dake Paris babban birnin kasar Faransa ta jingine shari’ar da akeyi wa tsohon shugaban kasar Jacques Chirac.Wannan bisa kalubalantar shari’ar da daga bangaren daya daga cikin lauyoyin kan hada shari’un na Chirac waje guda tun yana magajin garin birnin na Paris.Za a iya ci gaba da shri’ar idan alkali ya amince da ci gaba da daya daga cikin shari’un.Ana zargin tsohon shugaba Chirac da saka sunayen wasu abokan siyasarsa cikin ma’aikatan da ake biya, yayin da yake rike da magajin birnin na Paris. 

Tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac
Tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac