Faransa

Rikicin kan kudin garabasa na motocin Renault dake Faransa

Calos Ghosn, shugaban Renault - Nissan
Calos Ghosn, shugaban Renault - Nissan

Shugaban Kanfanin hada motocin Renault, Carlos Ghosn, ya ce yaki amincewa da bukatar mataimakin sa, na aje aiki, sakamakon abin kunya da aka samu, wajen mika asirin kanfanin ga wani kanfani na dabam.Shuagban kanfanin, ya ce shi da mataimakin nasa, ba zasu karbi kudin garabasar sun a wannan shekara ba, kuma kanfanin zai sake matakan tsaronsa.