FARANSA

Faransa ta yi fatar samun nasarar shiga Libya

Francois Baroin mai magana da  yawun gwamnatin kasar Faransa
Francois Baroin mai magana da yawun gwamnatin kasar Faransa Photo: Reuters/Philippe Wojazer

Bayan kawo karshen zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasashen Tunsiya da Masar ba tare da Faransa ta bayyana matsayinta cikin gaggawa ba, a yanzu haka kasar Faransa da Birtaniya ne suka bukaci Kwamitin Tsaro na Majalisar Dunkin Duniya kan daukar matakin soji don karya shugaban Libya Muammar gaddafi.Mai Magana da yawun Gwamnatin Faransa Francois Baroin, yace faransa wacce ta yi ruwa da tsaki wajen daukar wannan mataki zata bada gudummuwarta wajen daukar matakin soji kan kasar Libya.Mista Baroin yace daukar matakin sojin baya da nasaba da mallakar yankunan kasar Libya illa wani kokarin ne na kare al’ummar kasar Libya tare da karfafa masu kwarin gwiwar neman ‘yancinsu na karya gwamnatin Gaddafi.Sai dai kuma duk da cewa kasar Faransa da Birtaniya da Amurka sun amince da wannan matakin, sauran takwarorinsu China da Rasha da Jamus sun nisanta kansu ga matakin na Libya.Da dadewa dai an zargi kasar Faransa dangane da kame bakin ta game da zanga-zangar kasashen Tunisia da Masar al’amarin da yayi sanadiyar Michele Alliot-Marie, Ministar harakokin wajen kasar yin Murabus