Portugal ta shiga rudanin siyasa bayan Prime Minista yayi murabus
Wallafawa ranar:
Kasar Portugal ta abka cikin rudanin siyasa bayan da Prime Ministan kasar ya bayyana yin murabus sanadiyar wani sabani da ya samu da majalisar kasar don amincewa da sabon tsarinsa na farfado da tattalin arzikin kasar a daidai lokacin da kasashen turai ke shirin gudanar da taro don nazarin matsalar basussuka.A jiya laraba ne Prime Minista Jose Socrates ya mika takardar yin murabus dinsa tare da bayyana cewa ba zai iya ci gaba da shugabanci ba tare da samun goyon baya ba a daidai lokacin da ‘yan adawa suka ki amincewa da shirin Gwmanatinsa na tsuke bakin aljihu.A gobe juma’a ne dai shugaban kasar Anibal Cavaco Silva zai gana da Jam’iyyun kasar domin warware sabanin da aka samu a majalisar kasar. Ana dai tunanin shugaban zai bukaci jam’iyyun su kulla gwamnatin hadin gwiwa ko kuma ya yi watsi da majalisar don gudanar da wani sabon zabe.