Turai

Tarrayar turai na son kawo canji a game da VISA Schengen

Tutucin kasashen tarrayar Turai
Tutucin kasashen tarrayar Turai Getty Images

Komitin kungiyar tarrayar turai, zai gabatar da wani kuduri kan zirga-zirga da takardar izinin ta Schengen cikin yankunan da lamarin ya shafa.Komishinar harakokin cikin gidan kungiyar tarrayar turai,Cecilia Malmstrom za ta gabatar da wani kuduri kan maganar zirga-zirga da sa ido a cikin kasashen yankin da ke karkashin yarjajaniyar Schengen. Wanan sabon kuduri, da ke kumshe da kwaskwarima ga tsarin na issili da aka sani, ya samo tushe ne bayan kasar Faransa ta nuna kyamar shigar baki ‘yan kasar Tunisiya a kasar ta ,waanda kasar Italiya ta hannatama takardar izini zirga-zirga a yankin karkashin yardaidainiyar Schengen .Hujar da shugaban kasar ta Fransa Nicolas Sarkozy ya gabatar a game da wanan lamari ita ce :matsalolin da ake fuskanta game da samarma yan kasa aiki.A halin yanzu kishi 23 cikin100 na baki basu da aikin yi ,sai dai zaman kashe wando.Al’ummar kasar Fransa na karuwa da mutane dubu 110 duk shekara.A na gani Kasar Italia za ta yi bayani a cikin sati 2 nan gaba game da takardun izini da ta bada ga yan kasar ta Tunisiya.