Faransa

Ana ci gaba bikin nuna fina finai a Cannes dake Faransa

A ci gaba da bikin nuna fina finan duniya da ake yi a Cannes, dake kasar Faransa, Peter Fonda, tauraron shirin fina finan Easy Rider, na shekarar 1969, ya bayyana shugaba Barack Obama, a matsayin maci amana, kan yadda ya tafiyar kwararan man kanfanin BP, wanda aka samu kan tekun Mexico.Fonda ya ce, ya rubuta wasika ga shugaban, inda ya bayyana masa fushinsa kan lamarin, kan yadda ya bar 'yan kasashen waje, suka shiga kasar, suka kuma musu ta’adi. 

Bikin Cannes
Bikin Cannes REUTERS/Eric Gaillard