Turai

Toka daga aman wutar dutsi na janyo cikas wa jiragen sama a Turai

REUTERS/Ingolfur Juliusson

Tokar dake fita daga tsaunin dake aman wuta a kasar Iceland, na ci gaba da barazana ga sufurin jiragen sama, inda kanfanonin British Airways, KLM, Lingus da Easy Jet, duk suka soke zirga zirgan jiragensu jiya da yamma.Matsalar ta sa dole daren jiya, shugaba Barack Obama ya bar Ireland, zuwa Birtaniya, sabanin yadda aka tsara tafiyarsa.A wani labarin, kamfanin Jiragen saman KLM, na kasar Holland, ya dakatar da jigilar jiragensa shida, zuwa Birtaniya da Scotland, saboda tsoron tokar dake fita daga tsaunin dake aman wuta a kasar Iceland.Kakakin kanfanin, Ellen van Ginkel, ta ce an dakatar da tashin jiragen, sai zuwa yau da rana, domin nazarin yadda matsalar take.