Turai

Kungiyar G-20 za ta taro kan matsalar Fukushima

tambarin kungiyar kasashen G-20
tambarin kungiyar kasashen G-20 Reuters

Kasashen Kungiyar da suka fi habakar tattalin arziki a duniya, ta G-20, za su gudanar da wani taro a kasar Faransa, dan duba matsalar da aka samu ta tashar nukiliyar Fukushima, domin daukar matakan gyara.Tuni dai kasar Jamus ta bayyana shirin ta na rufe tashoshin nukiliyar ta, dan samun wasu sabbin dabarun samun makamashi.