Birtaniya

Cameron zai jagoranci taron gaggawa kan rikicin Birtaniya

Prime Ministan Birtaniya David Cameron
Prime Ministan Birtaniya David Cameron REUTERS/Parbul TV

Rikicin da ke ci gaba da bazuwa a sassan yankunan Birtaniya, Prime Ministan kasar David Cameron, ya katse hutunsa domin jagorantar taron gaggawa kan rikicin da aka kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanarwa.Rikicin wanda a yanzu haka ke ci gaba da bazuwa a yankunan Liverpool, da Bristol da Nottingham daLeeds da kuma Birmingham, a nan take ne David Cameron ya katse hutunsa da yake gudanarwa a Tuscany can yankin kasar Italiya.Tuni dai aka haramta gudanar da wasan sada zumunci da aka shirya gudanarwa tsakanin Ingila da kasar Netherland a yau Talata.Sama da mutane 400 ne, a yanzu haka aka cafke a birnin London.Rikicin kuma ya barke ne a Tottenham a karshen makon daya gabata, bayan bindige wani mutum da dan sanda yayi.