Faransa

Nafissatou na neman Strauss-Khan ya biya ta diyya

Naffissatou Diallo dake zargin Dominich Strauskhan da yi mata Fyade
Naffissatou Diallo dake zargin Dominich Strauskhan da yi mata Fyade Reuters/Shannon Stapleton

Nafissatou Diallo Ma'aikaciyar Otel da ta zargi tsohon Shugaban asusun bada lamuni na duniya Dominich Strauss-Khan da yunkurin yi mata fyade ta shigar da kara kotu domin a biya ta diyya.Nafissatou Diallo na neman kotu ta tursasawa Strauss Khan ya biyata diyya, saboda hari mai tsauri da ya kai mata.Tuni da Mista Strauss-Kahn ya musanta zargin da ake masa, inda yace Nafissatou ta yi zargin ne domin neman kudi.Har yanzu dai masu shigar da kara basu yanke shawarar sake gurfanar da Struss-Khan a gaban kuliya ba, kan aikata laifukan da ake zarginsa, saboda sabani da ake samu na bayanan da Nafissatou ke gabatarwa kotun.